Hausa Veterinarian

Hausa Veterinarian Shawarwari akan kula da lafiyar dabbobin mu domin kuwa kula da lafiyar dabbobin mu tamkar kula da lafiyar mu ne

Happy World Veterinary Day! 🌍 This year’s theme, “Animal Health Takes a Team,” hits home for me. Growing up on a livesto...
26/04/2025

Happy World Veterinary Day! 🌍

This year’s theme, “Animal Health Takes a Team,” hits home for me.

Growing up on a livestock farm, I saw how animals were often viewed primarily for their economic value. 💔 When they got sick, the solution was often slaughter, not treatment. My heart ached for them. 🥺That childhood experience sparked my passion for veterinary medicine and showed me how connected we all are.

Now, as a veterinarian and One Health advocate, I know that healthy animals = healthy people = a healthy planet.

💚Today, I’m celebrating all the amazing vets, epidemiologists, public health folks, and everyone working to make our world a healthier place for all beings. 🙌🏽 It truly takes a team! 💪🏽Let’s keep building bridges and working together. 🐾








                    I have been
21/11/2024



I have been

Ko kunsan dabi’un mu na shan magani yana taimakawa wajen hana magungunan da mukesha suyi aiki a jikin mu yanda ya kamata...
12/11/2024

Ko kunsan dabi’un mu na shan magani yana taimakawa wajen hana magungunan da mukesha suyi aiki a jikin mu yanda ya kamata???

Sanin kanmu ne cewar babu wani mutum wanda yana ji yana gani zaiyi abinda zai cutar da lafiyar shi da gangan saidai a bisa rashin sani…

Daga ciki akwai;

1. Shan magani yadda aka ga dama ba tare da tuntubar likita to ma’aikacin lafiya ba. Misali nice nake fama da ciwon kai, sai naje asibiti likita ya bani magani sai na sha har yayi saura, sai naji wata tana ciwon kai sai na dauka na bata sauran. Hakan ba daidai bane kuma ba lalle maganin yayi mata aiki ba saboda babu tabbacin cewa cutar da ta sakani nake jin ciwon kai iri daya ce da cutar da take damunta.

2. Rashin cika ka’idojin da aka bayar domin shan magani. Misali maganin da yakamata asha na saati sai asha na kwana 3, daga anji jiki ya fara samun sauki shikenan sai a ajiye adaina sha

3. Wuce ka’idar da aka bayar domin shan magani. Misali ance asha magani na kwana 3 sai mutum yasha na saati koma fiye da haka

12/11/2024
Jikin ko wanne mutum ko dabba ya kasance yana daukar magani a matsayin wani bako wanda ya zo domin kareshi daga miyagun ...
02/11/2024

Jikin ko wanne mutum ko dabba ya kasance yana daukar magani a matsayin wani bako wanda ya zo domin kareshi daga miyagun kwayoyin cuta. Idan wannan bakon ya shigo jiki a lokacin da jiki yake bukatar hakan, zai yi kokarin yin yaaki da wannan kwayoyin cutar domin kashe su kokuma nakasa su. Shi wannan bakon ya kasance yana yin yaakin ne a hankali a hankali ta hanyar bin matakai kala-kala ba wai lokaci daya ba. Haka zalika idan ya gama aikin shi, nan ma ba a lokaci daya yake tafiya ya bar jiki ba yana daukan lokaci kafin ya fita. To wannan lokacin da yake dauka kafin ya fita gaba daya shine “withdrawal period”

Yin gaggawa wajen yanka dabbobin mu da suke karkashin kulawar likita ko ma’aikacin lafiya batare da jiran “withdrawal period” ba, shi yake janyowa muci wannan sauran sinadaran magungunan a jikin nama, kuma hakan na iya jawo mana “AMR”

Dr Nusaiba Musa (DVM)
hausa_vatarinarian

Dafarko dai yakamata mu sani cewa bafa wai maganin da muke sha bane ya daina aiki ko kuma kamfani s**a rage mishi karfi ...
31/10/2024

Dafarko dai yakamata mu sani cewa bafa wai maganin da muke sha bane ya daina aiki ko kuma kamfani s**a rage mishi karfi kamar yanda yawancin mu muka dauka. 🤔


A halin yanzu ana fama da wani abu wai shi “Antimicrobial Resistance (AMR)” 💡

Shi wannan AMR yana faruwa ne lokacin da ƙwayoyin cuta na “bacteria” da “fungi” da “parasites” s**a daina karbar magungunan da ake amfani wajen kashe su ko rage yaduwar su ❌❌❌

Hakan yana faruwa ne sakamakon juriya da kwayoyin cutar s**a samu har ya kasance magungunan basu yin tasiri akansu. Kuma hakan yana kara haɗarin;
1. Yaduwar cututtuka masu wuyar magancewa
2. Rashin lafiya mai tsanani
3. Nakasa
4. Harma yakai ga mutuwa 😭

Ku biyoni a rubutuna na gaba domin sanin;
1. Wanne abubuwa ne suke jawo AMR?
2. Shikuma nama meye huruminshi a AMR?
3. Wacce gudun mawa zamu iya bayarwa domin dakatar da AMR

Mu rungumi manufar "Kiwon Lafiya Daya" ta hanyar sanin alaƙar da ke tsakanin lafiyar ɗan adam 👨‍👩‍👧‍👦, lafiyar dabbobi 🐈...
21/02/2024

Mu rungumi manufar "Kiwon Lafiya Daya" ta hanyar sanin alaƙar da ke tsakanin lafiyar ɗan adam 👨‍👩‍👧‍👦, lafiyar dabbobi 🐈🐕🐄, da lafiyar muhalli 🏡
Hakan yana da mahimmanci don samun lafiya mai dorewa da bunƙasa a gaba! 🌱🐾


"Lafiya daya"   shine yake nuna yadda lafiyar mutane, dabbobi, da muhalli ke hade. Idan muka kula da daya, muna taimakaw...
20/02/2024

"Lafiya daya" shine yake nuna yadda lafiyar mutane, dabbobi, da muhalli ke hade. Idan muka kula da daya, muna taimakawa wajen kula da sauran ne






28/09 World Rabies Day Protect yourself and your family by vaccinating your animals and you against the deadly virus    ...
28/09/2023

28/09 World Rabies Day

Protect yourself and your family by vaccinating your animals and you against the deadly virus

26/09/2023

- Idan kukaji bature yace *Zoonotic diseases* toh yana nufin cutar da mutum zai iya dauka daga jikin dabbobin shi kokuma...
01/08/2022

-

Idan kukaji bature yace *Zoonotic diseases* toh yana nufin cutar da mutum zai iya dauka daga jikin dabbobin shi kokuma dabba ta dauka daga jikin mai ita

🐈 Kuna da labarin Zoonotic Diseases?

🐕 Fada mana wadda kika/kasani a comment section

25/07/2022

Assalamu alaikum!

Ina muku barka da zuwa wannan shafin nawa mai suna *HAUSA VETERINARIAN*.

Na kirkiri wannan shafin ne domin bada shawarwari da fadakarwa da kuma wayar da kan al'umma akan lafiyar dabbobin mu da harshen hausa. Dukda nasan ba lallai ne komai ya fassaru da harshen hausa ba amma zan kamanta domin al'ummar mu su amfana.

Na lura akwai shafika masu kamanceceniya da wannan a kafofin sada zumunta kala kala amma da wuya kuga (ko kuma ma babu) wanda akeyi da hausa kuma akwai al'ummar mu da suke bibiyar shafikan sada zumunta da dama da basu iya harshen turanci ko faransanci ko makamancin su ba. Hakan ne ya sa nayi kwadayin bude wannan shafi dafatan zaku bani hadin kai.

Ina maraba da shawarwari domin kawo gyara da cigaban wannan shafi. Yananyi hadinkan da zan samu daga wajen ku shine zai bani kwarin gwiwar dorewa da wannan abu.

Bangaren tsokaci (comment section) a bude yake domin mu karu da juna. Amma don Allah banda yada jita-jita (rumor) ko damfarar juna (scam) ko zagin juna (insults and hate speech) da dai sauran su. Ina fatan zamu kare mutuncin juna tare da girmama juna

Nagode sosai!!! 🙏
Hausa Veterinarian ❤️

Address

Ring Road Eastern Bypass
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Veterinarian posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category