16/03/2026
DOMIN INGANTA SANA'ARKA TA KIWO.
Idan kana son inganta harkarka ta kiwo, dole ne ka fahimci cewa kiwo ba kawai saka dabbobi a gona ba ne. Kiwo sana’a ce da take bukatar tsari, hakuri, da bin ka’idoji. Duk wanda yake son ganin gonarsa ta yi kyau tare da samun nasara, dole ya dauki lokaci yana kula da dukkan abubuwan da s**a shafi kiwo.
Abin da ake yawan gani shi ne, wasu manoma suna yawan korafi da matsaloli a gonarsu. Wani zai ce kajinsa suna mutuwa, wani zai ce basa yin kwai, wani kuma zai ce yana kashe kudi amma baya ganin riba. Amma idan ka bincika sosai, za ka ga cewa mafi yawancin matsalolin suna faruwa ne saboda rashin kulawa da bin ka’idojin kiwo.
Misali, wasu basa kula da tsabtace gidan gona, alhali datti yana daya daga cikin manyan abubuwan da ke jawo cututtuka. Wasu kuma basa bin jadawalin allurai (vaccination) yadda ya kamata, wanda hakan kan sa kaji su kamu da cuta cikin sauki. Haka kuma akwai wadanda basa kula da ingancin abinci da ruwa, alhali wadannan abubuwa sune ginshikin wajen samar da lafiyar dabbobi.
Wani babban kuskure kuma shi ne rashin lura da alamar matsala da wuri. Idan manomi ya ga dabbarsa tana nuna wata alama ta rashin lafiya amma ya yi shiru, to yana iya jawo babbar asara a gaba. Amma idan aka lura da matsalar da wuri, sau da yawa ana iya shawo kanta kafin ta zama babbar matsala.
Saboda haka yana da kyau duk manomi ya rika tsayawa yana duba gonarsa da kyau.
Ka tambayi kanka:
Shin ina kula da tsafta yadda ya kamata?
Shin ina ba dabbobina ingantaccen abinci?
Shin ina bin jadawalin allurai?
Shin ina lura da duk wata alama ta matsala da wuri?
Idan ka rika yin wannan bincike a kai a kai, za ka ga cewa matsaloli suna raguwa sosai, kuma gonarka zata fara kawo maka riba kamar yadda kake so.
LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING ✍️