04/07/2026
LABARI MAI TAƁA ZUCIYA: Bayan Shekaru Na Kare Jagoransa, Yanzu Aikinsa Ya Zama Tsaron Gawar Shaheed Ali Khamenei (h).
Mutumin da ya shafe shekaru yana sadaukar da rayuwarsa domin kare Shaheed Ayatollah Ali Khamenei, yau yana tsaye cikin jimami yana tsaron gawar jagoran da ya rantse zai kare da ransa.
Masana harkokin tsaro kan ce, babu wani lokaci da ya fi nauyi ga mai tsaron lafiyar shugaba kamar lokacin da ya rasa mutumin da ya dauki rayuwarsa gaba ɗaya yana karewa.
Hoton mai tsaron lafiyar yana tsaye cikin baƙin ciki ya zama abin da ya taɓa zukatan mutane da dama, yayin da Iran ke ci gaba da shirye-shiryen jana'izar marigayin